Jump to content

Springbok Legion

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Springbok Legion
Bayanai
Ƙasa Afirka ta kudu

Ƙungiyar Springbok Legion kungiya ce ta tsoffin sojoji kuma kungiyar yaƙi da mulkin nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.[1][2]

An kafa ƙungiyar Springbok Legion a cikin shekarar 1941.[1][3] A cikin shekarar 1944, ƙungiyar ta zo ƙarƙashin jagorancin Jack Hodgson da Jock Isacowitz.[1]

Domin babban zaɓe na shekarar 1948 na Afirka ta Kudu, ƙungiyar Springbok Legion ta ƙarfafa 'yan Afirka ta Kudu masu launin fata su zaɓi jam'iyyar United Party da Labour Party.[4] Springbok Legion tayi la'akari da ƙoƙarin jam'iyyar National Party don ƙara hana 'yan Afirka ta Kudu masu launin fata da kuma mayar da mulkin demokraɗiyya na Afirka ta Kudu a matsayin mai kama da farkisanci ko kama-karya.[5] Bugu da ƙari, ƙungiyar ta kasance ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu yawa waɗanda suka yi adawa da kuma turjiya da Mummunar Dokar Kwaminisanci.[6][7]

A shekarar 1952, Rundunar Springbok tana da mambobi 125,000. A waccan shekarun taron Springbok Legion, an zaɓi Cecil Williams a matsayin shugaba. [8] Williams ya yi aiki tare da Bram Fischer don haɗa ƙungiyar tare da Congress of Democrats, amma kafin ƙungiyoyi su haɗu, 'yan sanda sun kai hari ofisoshin Springbok Legion kuma Ministan 'yan sanda ya umurci Williams da ya yi murabus daga kowace ƙungiya da ya kasance memba. [8]

Fighting Talk

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin watan Janairun shekarar 1942, Homefront League of the Springbok Legion legion ta kaddamar da jaridar Fighting Talk, wanda aka kaddamar a Johannesburg. Ana buga Fighting Talk kowane wata a cikin harshen Ingilishi da Afirkaans.[8]

Gwamnatin mulkin nuna wariyar launin fata ta ruguza Fighting Talk da karfi a watan Fabrairun shekarar 1963.[8]

  1. 1.0 1.1 1.2 Samfuri:Harvp
  2. Samfuri:Harvp
  3. Samfuri:Harvp
  4. Samfuri:Harvp
  5. Samfuri:Harvp
  6. Samfuri:Harvp
  7. Samfuri:Harvp
  8. 8.0 8.1 8.2 8.3 "Cecil Williams". South African History Online. 21 October 2011. Retrieved 29 January 2025.

Ayyukan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]

Ƙara karantawa

[gyara sashe | gyara masomin]